Tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya bai wa sabon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wa’adin sa’o’i 48 domin ya janye wasu kalamai da ya danganta masa tare da ba shi haƙuri a bainar jama’a, ko kuma ya fuskanci matakin shari’a.
Wannan na cikin sanarwar da Mustapha Rabiu Kwankwaso, wanda shi ne Mataimakin ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, ya fitar domin mayar da martani kan wasu zarge-zargen da ya ce kwamishinan ya yi a kansa.
Mustapha ya bayyana cewa Sanusi Bature ya zarge shi da zuwa cibiyoyin gyaran hali da dama a ƙasashen duniya, tare da yin iƙirarin cewa mahaifinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kafa Cibiyar Gyaran Hali ta Kiru ne saboda shi.
Ya musanta waɗannan zarge-zarge, yana mai bayyana su a matsayin ƙarya da yunƙurin ɓata masa suna domin karkatar da hankalin al’ummar Kano daga muhimman batutuwan da suka shafi gudanar da gwamnati.
