Wasu fursunoni biyu da aka yanke wa hukuncin laifi sun tsere daga gidan gyaran hali na Okene da ke jihar Kogi, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka fara farautarsu domin sake cafke su.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026, kamar yadda wani rahoton rundunar ‘yan sanda daga sashen Okene ya nuna.
An bayyana sunayen fursunonin a matsayin Samson David, wanda aka yanke wa hukuncin laifin sata, da kuma Salvation Moro, wanda ke zaman gidan yari bisa laifin fashi da makami.
Rahoton ya ce jami’in da ke kula da gidan gyaran halin ne ya sanar da ‘yan sanda ta wayar tarho game da tserewar fursunonin da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar Lahadi.
Bayanan farko sun nuna cewa fursunonin sun tsere ne ta bayan katangar gidan gyaran halin.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an haɗa hotunan fursunonin cikin saƙon da aka aika wa ‘yan sanda domin taimakawa wajen gane su da kuma gano inda suke.
Rahoton ya ce: “Ana ci gaba da ƙoƙarin gano fursunonin da suka tsere domin sake cafke su.”
