
Aminu Abdullahi Ibrahim
Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano mai kula da harkokin ilimi, Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni, ya ce duk da cewa Najeriya na samun ci gaba a wasu ma’aunai na tattalin arziki, hakan bai haifar da gagarumin sauƙi a rayuwar talakawa ba.
Farfesa Tsauni ya bayyana haka ne a wani taro da ƙungiyar Non-Formal Development for Education and Health Initiative ta shirya, mai taken “Nigeria at a Crossroad: Who Is to Fix It?”

Ya ce an samu ɗan ci gaba a yawan kayayyaki da ayyukan da ake samarwa a ƙasar, wato GDP, da kuma wasu alamomin tattalin arziki, amma waɗannan nasarori ba su haifar da raguwar talauci yadda ya kamata ba.
Mataimakin shugaban jami’ar ya jaddada cewa magance matsalolin Najeriya bai kamata a ɗora wa gwamnati ko shugabanni kaɗai ba. Ya ce kowane ɗan ƙasa na da rawar da zai taka wajen farfaɗo da ƙasar.
Ya kuma buƙaci gwamnati ta tsara tare da aiwatar da manufofin da za su kawo sauyi a zahiri, tare da gina amincewar jama’a.

A nasa jawabin, babban mai baiwa kungiyar data shirya taron NDEHI shawara, Dakta Auwal Halilu, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi kishin ƙasa, gaskiya da riƙon amana, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.

