Gwamnatin Kano ta sha alwashin biyan dukkan kuɗaɗen fansho da ta gada da kuma waɗanda suka taru daga shekarar 2019 zuwa yanzu, waɗanda yawansu ya kai naira biliyan 42, tsakanin watan Nuwamba da muke ciki zuwa ƙarshen watan Afrilu mai zuwa.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwar jihar karo na 42, wanda aka gudanar daga tsakar daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin.
Kwamshinan ya ce gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da biyan haƙƙin ’yan fansho, waɗanda suka kwashe lokaci suna jiran kuɗaɗensu, tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na biyan bashin da ta gada.
Kwamishinan ya ƙara da cewa shirin biyan kuɗaɗen zai gudana ne daga watan Nuwamba zuwa ƙarshen Afrilu, wanda hakan ke nufin gwamnatin za ta kammala biyan bashin wata guda kafin cikar wa’adin mulkinta na farko.
Wakilinmu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa gwamnatin Kano ta sake jaddada aniyarta na biyan dukkan kuɗaɗen fansho da ake bin ta, a wani yunƙuri na tabbatar da walwalar tsofaffin ma’aikatan gwamnati da kuma biyan su haƙƙoƙinsu.
