Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA) da Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa (NARD) sun yi watsi da wani tanadi a kudirin gyaran dokar lafiya ta ƙasa, wanda ke neman hukunta asibitoci da ma’aikatan lafiya da suka ƙi kula da marasa lafiya a yanayin gaggawa.
Kudirin ya tanadi hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari ko tarar naira dubu 300 ga waɗanda suka karya ƙa’idojin kula da marasa lafiya na gaggawa.
Ƙungiyoyin sun nuna rashin amincewarsu da matakin, tare da yin barazanar shiga yajin aikin gama-gari a faɗin Najeriya idan ba a janye ko sauya tanadin ba.
Sai dai kudirin bai zama doka ba tukuna, yayin da ake ci gaba da muhawara kan yadda za a tabbatar da cewa marasa lafiya sun samu kulawar gaggawa ba tare da tauye haƙƙin ma’aikatan lafiya ba.
