Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ware tallafin Naira miliyan 100 ga ’yan kasuwar kifin Yankifi da gobara ta shafa, tare da bayar da umarnin sake gina sassan kasuwar da gobarar ta lalata domin dawo da harkokin kasuwanci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jajantawa da ya kai kasuwar ranar Juma’a, bayan gobarar da ta tashi a daren Lahadi, inda ta lalata kifaye masu yawa, na’urorin sanyaya kaya da sauran muhimman kadarorin ’yan kasuwar da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.
Abba Yusuf ya bayyana gobarar a matsayin babban rashi ba ga ’yan kasuwar kawai ba, har ma da al’ummar Kano baki ɗaya, musamman duba da muhimmancin kasuwar wajen samar da kifaye da tallafa wa harkokin kasuwanci da rayuwar jama’a.
Ya kuma buƙaci waɗanda lamarin ya shafa da su yi haƙuri tare da dogaro ga Allah, yana mai kira ga shugabannin kasuwar da masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa matakan kariya domin kauce wa sake afkuwar irin wannan ibtila’i.
Gwamnan ya ce za a fitar da tallafin Naira miliyan 100 cikin mako guda ta hannun ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha da Kwamishinan Zuba Jari da Kasuwanci, yayin da ya umarci Kwamishinan Ayyuka da ya tsara yadda za a sake gina sassan kasuwar da gobarar ta shafa.
