Sama da mutum dubu 600,000 ne shirin ROOTS na ƙungiyoyin AHIP da IOM ya wayar wa da kai kan haɗarin ƘAURA ƙasashen ƙetare ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙarfafa gwiwar mata da matasa kan dabarun sana’o’i da noma domin su dogara da kansu maimakon shiga haɗarin tafiye-tafiyen da ka iya jefa rayuwarsu cikin barazana.
A jawabin ta yayin taron, shugabar shirin ROOTS na AHIP, Halima Kasim Usman, ta ce shirin na ƙarfafawa mata da matasa da kuma sauran masu rauni ta hanyar samar musu da hanyoyin samun kuɗin shiga, tare da wayar da kan jama’a kan dokokin ECOWAS na zirga-zirgar mutane tsakanin ƙasashe cikin ’yanci, domin rage safarar mutane da ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.
Shirin wanda ya gudana a Kano, ya kuma samar da tallafi ga mata manoma, ’yan ƙananan kasuwanni waɗanda suka dawo daga ƙaura, ’yan gudun hijira da matasan da ke fuskantar barazanar yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, ta hanyar koyar da su dabarun noma masu jure sauyin yanayi da sauran sana’o’in dogaro da kai.
Wani daga cikin mahalarta taron wanda ya taɓa yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba Habibu Abdullahi daga Dakata, ya bayyana yadda ya bi ta hamadar Sahara zuwa Libya da niyyar isa Spain, yana mai cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan tafiya.
Ita ma Binta Auwalu daga Dawakin Kudu, ta ce ta fuskanci cin zarafi da wahalhalu a lokacin tafiyarta zuwa Nijar, inda wani fasinja ya mutu sakamakon cunkoson motar da suke ciki, aka kuma yi zargin an bar gawarsa a hamadar Sahara.
A nasa jawabin, wakilin Dagacin Bunkure, Alhaji Aminu Bunkure, ya ce horar da al’ummar yankin kan dabarun noma da raba musu ingantattun iri ya taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, inda mata suka rungumi noman lambuna da amfani da kwantena a gidajensu.
Shi ma Maijidda Dalhatu na hukumar NOA, ya buƙaci iyaye su koyar da ’ya’yansu sana’o’in dogaro da kai da kyawawan ɗabi’u, yayin da Farfesa Amina Lawan Mustapha ta Jami’ar Bayero Kano ta ce ilimin da aka ba mata kan noma, adana amfanin gona da tallata shi zai taimaka wajen inganta tattalin arzikinsu.
