Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC, sun yi alƙawarin haɗin gwiwa da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da amfani da motocin agajin gaggawa 484 da gwamnatin Kano ta raba yadda ya kamata.
Kwamishinan hukumar ICPC mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Barista Ahmad Muhammad Wada, ne ya bayyana hakan a madadin hukumomin biyu, yayin bikin ƙaddamar da motocin a filin wasa na Kano Pillars.
Wada ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da almundahana, amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba ko wata ɗabi’a da ta saɓawa ƙa’idojin kula da motocin, zai fuskanci matakin da ya dace, yana mai jaddada muhimmancin riƙon amana wajen kula da dukiyar al’umma.
Hukumomin sun bayyana cewa haɗin gwiwarsu zai taimaka wajen kare dukiyar al’umma da kuma tabbatar da cewa shirin ya cimma manufar da aka samar da shi.
