Wata babbar kotun tarayya da ke Warri a Jihar Delta ta soke takarar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, a matsayin dan takarar jam’iyyar NDC mai wakiltar Delta Central a zaben 2027.
Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Hyeladzira Ajiya Nganjiwa, ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta cire sunan Omo-Agege daga cikin jerin sunayen ‘yan takarar zaben.
Hukuncin ya biyo bayan karar da Farfesa Alexander Osondu Akpodiete ya shigar, inda ya kalubalanci sahihancin takarar Omo-Agege, musamman kan kasancewarsa cikakken dan jam’iyyar NDC da cancantarsa ta shiga zaben fidda gwani.
Kotun ta gano cewa jam’iyyar NDC ta karya tanade-tanaden dokar zabe, saboda ba ta saka sunan Omo-Agege cikin rajistar mambobinta da ta gabatar wa INEC a kalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaben fidda gwani ba.
Haka kuma, kotun ta yi la’akari da cewa Omo-Agege ya halarci zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a ranar 18 ga Mayun 2026, kafin daga bisani ya koma NDC.
Alkalin ya kuma yi watsi da korafe-korafe biyar da Omo-Agege, NDC da INEC suka gabatar na neman a yi watsi da karar.
Kotun ta ce wa’adin da doka ta tanada na gudanar da sabon zaben fidda gwani ya riga ya wuce, lamarin da ka iya hana NDC sake tsayar da wani dan takara a kujerar Sanatan Delta Central a zaben 2027.
