Hukumar wayar da kan al’umma ta ƙasa NOA ta ce za ta ƙarfafa ayyukan wayar da kan jama’a da ilimantar da masu zaɓe a faɗin Najeriya cikin makonni shida masu zuwa, a wani mataki na shirye-shiryen zaɓukan shekarar 2027.
Shugaban hukumar, Malam na ƙasa malam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron horas da dabarun gudanarwa da ya haɗa manyan jami’an hukumar daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.
Malam Issa ya ce hukumar na shirin kawo sababbin tsare-tsaren gudanarwa domin inganta ayyukanta, ciki har da kafa kwamitocin wayar da kan jama’a kan kyawawan ɗabi’u a dukkan jihohi 36 da Abuja,
Lanre ya ce hukumar za ta fara amfani da tsarin sa ido kan kafafen yaɗa labarai a lokaci guda, domin bibiyar yadda ake yaɗa tallace-tallacen wayar da kai da sanarwar a gidajen rediyo, talabijin da jaridu, domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen amfani da kuɗaɗen gwamnati.
Taron ya kuma tattauna batutuwan ilimantar da masu zaɓe, wayar da kan al’umma tun daga tushe da kuma rawar da hukumar za ta taka a zaɓen 2027, tare da ƙaddamar da motar aiki da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa ofishin hukumar na jihar Kano domin ƙarfafa ayyukanta.
