Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙara albashin alƙalan manyan kotunan ƙasar da kashi 300 cikin 100, a wani mataki da ya ce zai taimaka wajen inganta walwalarsu da gudanar da ayyukansu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, inda ya jaddada muhimmancin samar wa alƙalai isassun kuɗaɗen gudanar da rayuwarsu domin su iya yin aikinsu ba tare da matsin tattalin arziki ba.
Shugaban ya ce ƙarancin albashi na iya jefa alƙalai cikin jarabawar karɓar cin hanci, yana mai bayyana cewa ba za a iya tsammanin samun cikakken adalci ba idan masu yanke hukunci na fama da matsalolin rayuwa.
Ya kuma bayyana ɓangaren shari’a a matsayin mafakar ƙarshe ta talaka, yana mai gargaɗin cewa duk wata matsala da ta raunana tsarin shari’a na iya shafar dimokuraɗiyyar ƙasar.
Tinubu ya ce inganta walwalar alƙalai na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin ƙarfafa tsarin shari’a da tabbatar da adalci.
