Hukumar Kwastam ta Najeriya ta dakatar da horas da sabbin ma’aikata 3,852 da ta ɗauka aiki, sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakaninta da Hukumar Kula da Daidaiton Ɗaukar Ma’aikata ta Tarayya.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne domin ba da damar ci gaba da tattaunawa kan zargin kura-kuran da aka samu a tsarin ɗaukar ma’aikatan.
A wata sanarwa da kakakin Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana cewa ɓangarorin biyu sun amince su warware takaddamar ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.
Takaddamar ta shafi zargin cire wasu mutanen da sunayensu suka fito cikin jerin waɗanda suka yi nasara, yayin da aka gayyaci wasu da ba su cikin jerin domin halartar horaswar.
Rahotanni sun kuma yi zargin cewa an samu ƙorafe-ƙorafe daga masu neman aikin da suka ce an cire su duk da kammala matakan tantancewa, ciki har da gwajin lafiya.
A watan Yulin 2026 ne Kwastam ta fitar da sunayen mutane 3,852 da suka yi nasara, daga cikin sama da mutum 573,000 da suka nemi aikin tun bayan fara tallata shi a watan Disambar 2024.
An fara horas da waɗanda suka yi nasarar ne a ranar 9 ga Oktoban 2026, kafin sanarwar dakatarwar, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin warware takaddamar.
