Masana harkokin noma a Najeriya sun bayyana cewa shirin gwamnatin tarayya na fitar da hatsin da ta adana a rumbun ajiyarta na iya taimakawa wajen rage tsadar kayan abinci, muddin an aiwatar da shi yadda ya kamata.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar gwamnatin tarayya na shirin sakin hatsin da ta adana, a wani mataki na sauƙaƙa wa jama’a samun abinci da rage matsin tattalin arziki.
Wani malami a Jami’ar Northwest da ke Kano, Malam Umar Musa Umar, ya bayyana cewa gwamnatoci na tanadin abinci a rumbunan ajiya domin tunkarar matsalolin da ka iya haddasa ƙarancin abinci, ciki har da fari da rashin tsaro.
Sai dai malamin ya yi gargaɗin cewa mayar da shirin wata hanyar siyasa ko neman goyon bayan jama’a na iya haifar da illa ga manoma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma.
Ya ce duk da cewa sakin hatsin na iya taimakawa wajen rage farashin abinci, akwai buƙatar a aiwatar da shirin cikin tsari domin kauce wa jefa manoma cikin asara.
Malam Umar Musa Umar ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da adalci wajen fitar da hatsin, tare da ɗaukar matakan tallafa wa manoma tun kafin fara damina.
Masana na ganin cewa yadda za a aiwatar da shirin da kuma lokacin da za a fitar da hatsin na daga cikin abubuwan da za su iya tasiri kan farashin kayan abinci a kasuwanni.
