Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirin daukar nauyin karatun ɗalibai 200 a Jami’ar Baba Ahmad da ke Kano a kowace shekara, tare da ware tallafi na musamman ga ɗalibai 50 da suka kammala karatu da ƙwarewa a jami’ar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyu na jami’ar, inda ɗalibai 310 suka kammala karatu a fannoni 11 na digiri na farko a zangon karatu na shekarar 2025/2026.
Gwamna Abba ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi, tallafawa ɗalibai masu hazaka da kuma ƙarfafa ingancin harkokin ilimi a Kano.
Tun da farko, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Idris Tanko, ya bayyana cewa ɗalibai 26 ne suka samu matakin digiri na farko wato First Class, inda mata 21 ke cikin waɗanda suka samu nasarar.
Farfesa Idris ya ce Amina Musa Abubakar, daga sashen nazarin sinadarai masu rai (Biochemistry), ce ta zama ɗalibar da ta fi kowa ƙwarewa, bayan samun maki 4.95 cikin 5, inda ya ce ɗalibai 168 sun fito daga tsangayar Kimiyya da Fasahar Kwamfuta, yayin da 142 suka fito daga tsangayar Kimiyyar Zamantakewa da Gudanarwa.
Farfesa Tanko ya kuma bayyana cewa Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta amince da shirin karatun Digiri a fannin Laifuka da Tsaro, yayin da jami’ar ke jiran amincewar ƙarshe daga Hukumar Kula da Ilimin Shari’a domin fara karatun Digiri a fannin Shari’a.
