Al’ummar Faransa sun sake fita kan tituna a ranar Asabar domin gudanar da zanga-zanga a mako na 6 a jere, inda suke buƙatar inganta ayyukan gwamnati, ƙarin albashi, da kuma nuna fushinsu kan tsadar rayuwa.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta bayyana cewa adadin masu zanga-zangar ya ragu sosai idan aka kwatanta da makonnin baya, inda ta ƙiyasta cewa mutane dubu 82 da 500 ne suka fito a faɗin ƙasar a wannan Asabar ɗin, sabanin mutane dubu 106 da suka fito a makon da ya gabata.
Sai dai ƙungiyoyin kwadago da masu shirya zanga-zangar sun ce adadin ya kai mutane 150,000 a duk faɗin ƙasar, wanda shi ma ya ragu daga 200,000 a makon jiya da kuma 800,000 a ranar 17 ga watan Oktoba.
Zanga-zangar dai ta samo asali ne tun a tsakiyar watan Satumba daga ɗaliban sakandare da ke buƙatar inganta yanayin karatu, kafin ta rikiɗe zuwa babbar zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa, rashin daidaito, da kuma cin zarafin al’umma da ƴansanda ke yi a ƙasar.
