Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Obafemi George, ya nuna shakku kan yiwuwar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya samu ƙuri’u miliyan 25 a Arewa maso Yamma a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
George, wanda ke cikin sashen yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise Television a ranar Alhamis.
Ya ce yana da wuya Atiku ya samu irin wannan goyon baya, ganin cewa ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, Abba Atiku Abubakar, ya sauya sheƙa zuwa APC, tare da bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jigon na APC ya ce rashin samun goyon bayan ɗan Atiku na jefa ayar tambaya kan ƙarfin goyon bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ke ikirarin samu a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
George ya kuma yi magana kan jam’iyyar ADC, inda ya yi zargin cewa ‘yar shugaban jam’iyyar na ƙasa, David Mark, mai suna Odon Odon, na neman takarar kujerar Majalisar Wakilai a Jihar Benue ƙarƙashin jam’iyyar APC.
A cewarsa, waɗannan sauye-sauyen siyasa na nuna ƙalubalen da ‘yan adawa za su fuskanta a zaɓen 2027, yana mai bayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu.
Atiku dai shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairun 2027, yayin da Tinubu ke neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin APC
