
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Kula da Makarantun Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano (KSPVIB) ta sanar da rufe makarantar Prime College da ke titin Alu Avenue, unguwar Nassarawa GRA a Kano, na tsawon mako biyu, sakamakon gazawar makarantar wajen bin umarnin hukumar na sabunta da kuma sake tantancewa takardar shaidar izinin gudanar da ayyuka (Certificate of Operations).
Sakataren zartarwa na hukumar, Kwamared Baba Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, 2026, inda ya ce matakin rufe makarantar zai fara aiki daga ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2026.
Ya bayyana cewa hukumar ta dauki matakin ne bayan makarantar ta ci gaba da kasa bin ka’idojin da aka gindaya mata, duk da cewa an aika mata da sanarwa da gargadi a hukumance sau da dama, tare da ba ta isasshen lokaci domin gyara matsalolin da ke gabanta.
A cewar sakataren zartarwar, dokokin jihar Kano sun wajabta wa dukkan makarantun masu zaman kansu da na sa-kai mallakar ingantacciyar takardar shaidar izinin gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da cewa takardar tana nan cikin inganci a kowane lokaci.
Ya ce sauran makarantu a fadin jihar sun bi wannan umarni, inda suka nemi tare da samun takardun shaidar, saboda haka babu dalilin da zai sa Prime College ta zama kebantacciya ko ta kauce wa wannan doka.
Kwamared Baba Abubakar Umar ya kara da cewa, bai kamata a rika yi wa wata makaranta sassauci ko mu’amala ta musamman ba, domin hakan zai saba wa ka’idojin bin doka da oda. Ya jaddada cewa babu wata makaranta da ta fi karfin doka, kuma babu wanda za a kebe daga bin ka’idojin hukumar.
Ya ce matakin ya yi daidai da sashe na 16, karamin sashe na 2, na dokar kafa Hukumar Kula da Makarantun Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano mai lamba 2 ta shekarar 2026, kamar yadda aka yi wa dokar gyara.
Sakataren zartarwar ya bayyana cewa manufar rufe makarantar na tsawon mako biyu ita ce bai wa mahukuntanta wata dama ta karshe domin cika dukkan sharuddan da ake bukata da kuma daidaita matsayinta da dokokin hukumar.
Ya kuma yi gargadin cewa idan har makarantar ta gaza bin umarnin hukumar cikin wa’adin mako biyun da aka ba ta, za ta iya fuskantar wasu karin takunkumai, ciki har da rufe ta gaba daya.
A wani bangare na jawabin, sakataren zartarwar ya jaddada cewa matakin da hukumar ta dauka ba na nuna wariya ba ne, ba tsoratarwa ba ne, kuma ba wata ramuwar gayya ta kashin kai ba ce, illa kokari ne na tabbatar da bin doka, adalci da kuma samar da daidaitattun ka’idoji ga dukkan makarantu.
Ya ce hukumar na da alhakin kare dalibai, inganta ingancin ilimi da kuma tabbatar da cewa dukkan makarantun da ke aiki a jihar suna bin dokokin da aka shimfida.
Ya yi kira ga masu makarantun masu zaman kansu da na sa-kai da su hada kai da hukumar tare da cika dukkan wajibai da dokokin jihar suka dora musu.
Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin adalci da tsayin daka, ba tare da tsoro ko nuna fifiko ga wani bangare ba, yana mai jaddada cewa babu makarantar da ta fi karfin doka a Jihar Kano.
