Rundunar ’yan sandan jihar Kogi ta musanta zargin cewa ana horas da wasu mutane amfani da bindigogi domin harkokin siyasa a ƙaramar hukumar Ankpa.
Kakakin rundunar, Salisu Afusat, ta ce horaswar ta kwanaki huɗu halastacciya ce, wadda hukumar sa-kai ta jihar ta shirya domin koyar da jami’an tsaron ma’adinai da iyakokin jihar sarrafa makaman da aka saya musu.
Ta ƙara da cewa an sanar da hukumomin tsaro kafin fara atisayen, tare da gargaɗin jama’a kan yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba domin kauce wa haddasa fargaba.
