Cristiano Ronaldo ya yi ritaya daga tawagar Portugal bayan shekaru 23: Tarihin da ba zai gushe ba
Tafiya mai cike da tarihi, nasarori da kafa tarihi ta zo ƙarshe!
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya sanar da yin ritaya daga wakiltar tawagar ƙasar Portugal, bayan shafe shekaru 23 yana kare martabar ƙasarsa a fagen ƙwallon ƙafa.
Tafiyar Ronaldo a tawagar Portugal ta fara ne a ranar 20 ga Agustan 2003, lokacin yana ɗan shekara 18 kacal, inda ya fara buga wa ƙasar wasa a karawar da ta yi da Kazakhstan.
Tun daga wannan lokacin, ya zama ɗaya daga cikin ginshiƙan tawagar, inda ya taimaka mata kaiwa wasan ƙarshe na EURO 2004, kafin daga bisani ya jagorance ta zuwa lashe kofin nahiyar Turai na farko a tarihinta a shekarar 2016.
Ya kuma taimaka wa Portugal lashe kofunan UEFA Nations League a shekarun 2019 da 2025.
A cikin shekaru 23 da ya shafe yana wakiltar ƙasarsa, Ronaldo ya buga wasanni 234, inda ya zura ƙwallaye 146, wanda ya sanya shi zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan buga wa tawagar ƙasa wasa tare da zura ƙwallaye a tarihin ƙwallon ƙafa na maza.
Ya kuma kafa wasu muhimman tarihi, ciki har da kasancewa ɗan wasa na farko da ya zura ƙwallaye a gasannin cin kofin duniya guda shida.
Bayan sanarwar ritayar tasa, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal ta bayyana aniyarta ta shirya masa gagarumin bikin bankwana, domin karrama irin gudummawar da ya bayar ga ƙasar.
Amma yaya tafiyar Ronaldo ta kasance tun daga fara buga wa Portugal wasa? Waɗanne tarihin ya kafa, waɗanne kofuna ya lashe, kuma wane matsayi ya bar wa ƙasar?
Mun tattara cikakken tarihin tafiyarsa, manyan nasarorinsa da abubuwan da suka sanya sunansa zama ɗaya daga cikin fitattun sunaye a tarihin ƙwallon ƙafa.
Karanta cikakken rahoton a shafinmu:
