Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ayyana neman mutane tara bayan sun ƙi amsa gayyatar da aka yi musu domin bincike kan zargin barazanar kashe Manajan Daraktan First Bank, Olusegun Alebiosu.
Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mashood Olohundare Jimoh, ya ce an kai wani kunshi gidan shugaban bankin, wanda aka yi masa kwalliya tamkar kyauta, amma aka gano harsasai biyu masu rai a cikinsa.
A cewar rundunar, binciken farko ya haɗa lamarin da takaddamar karɓar basussukan banki, inda ake zargin wasu kwastomomi sun yi wa shugaban bankin barazana.
Daga cikin mutane goma da aka gayyata domin amsa tambayoyi, mutum ɗaya ne ya bayyana, yayin da sauran tara ba su zo ba
. ‘Yan sanda sun nemi jama’a su bayar da bayanai kan inda mutanen suke, tare da jaddada cewa binciken na ci ga
