Masu bincike sun gano wasu gutsuttsuran tsoffin itatuwa da ake zargin sun kai shekaru kusan 4,300 a wani wuri da ake alakanta shi da jirgin Annabi Nuhu, a gabashin ƙasar Turkiyya.
An gano itatuwan ne a wani wuri mai siffar jirgin ruwa da ake kira Durupinar Formation, kusa da Dutsen Ararat, wanda ya shafe shekaru yana jan hankalin masu bincike da masu nazarin tarihi da addinai.
Wani rahoto da jaridar Express ta Birtaniya ta wallafa ya ce an samo gutsuttsuran itatuwan ne a zurfin sama da ƙafa 30 a ƙarƙashin ƙasa yayin gudanar da bincike a wurin.
Sakamakon gwajin farko da aka gudanar ya nuna cewa wani ɓangare na itacen na iya kasancewa daga tsakanin shekarun 2410 zuwa 2269 kafin haihuwar Annabi Isa, inda gwajin ya ba wannan hasashe damar kashi 60.6 cikin 100.
Wannan lokaci ya yi kusa da lokacin da wasu fassarorin littafan addini ke dangantawa da ambaliyar ruwan da aka yi a zamanin Annabi Nuhu.
Andrew Jones, wanda ya kafa aikin binciken , ya ce sakamakon farko ya yi daidai da wasu fahimtar gargajiya game da lokacin aukuwar ambaliyar ruwan da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.
Farfesa Cenker Atila, wanda ke jagorantar binciken, ya bayyana farin cikinsa bayan da ya samu damar riƙe gutsuttsuran itatuwan da aka gano.
“Na ji farin ciki matuƙa a lokacin da na fara fitar da itacen daga ƙasa na riƙe shi a hannuna. Tun da mun same shi a wani zurfi mai yawa, nan take na fahimci cewa da wuya ya kasance wani abu ne na zamani,” in ji shi.
Ya ce yiwuwar kasancewar itatuwan wani ɓangare na jirgin Annabi Nuhu na da matuƙar muhimmanci a gare shi.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa itatuwan na cikin jirgin Annabi Nuhu ba.
Masana ilimin ƙasa da dama sun bayyana cewa wurin na Durupinar wani tsarin halitta ne da ya samu sakamakon zaizayar ƙasa, ba ragowar wani tsohon jirgin ruwa ba.
Masu gudanar da binciken sun ce har yanzu suna buƙatar ƙarin nazari domin gano yadda itatuwan suka shiga ƙarƙashin ƙasa da kuma ainihin shekarunsu.
Andrew Jones ya ce tawagarsa na ci gaba da nazarin bayanan da aka samu kafin yanke hukunci.
Ya ce, “Abin da har yanzu ba mu sani ba shi ne yadda itacen ya shiga wurin.”
Ya kuma bayyana cewa ana sa ran samun ƙarin sakamakon gwaje-gwaje a watan Disamban 2026.
Wurin na Durupinar, wanda tsawonsa ya kai kusan mita 157, an fara gano shi ne a shekarar 1959 ta hanyar hotunan sama.
Siffarsa mai kama da jirgin ruwa da kuma kusancinsa da Dutsen Ararat sun jawo ce-ce-ku-ce tsawon shekaru dangane da yiwuwar kasancewarsa wurin da jirgin Annabi Nuhu ya tsaya, kamar yadda wasu bayanai suka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki.
Duk da wannan sabon bincike, har yanzu babu cikakkiyar hujjar kimiyya ko matsayar masana da ta tabbatar da gano jirgin Annabi Nuhu a wurin.
Madogara: Jaridar Express ta Birtaniya.
