Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya samu tabbacin goyon bayan shugabannin al’ummar Igbo da ke zaune a Kano ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Shugabannin na al’ummar Igbo sun bayyana matsayarsu ne yayin wata ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Igbo na Kano, Igwe Boniface Igweke, Eze Dioramma na huɗu, inda suka ce sun cimma matsaya ta haɗin kai tare da shawo kan rarrabuwar kawunan da ta faru a tsakaninsu a zaɓen 2023.
Sun kuma yabawa gwamnatin jihar bisa samar da tsaro da yanayin zaman lafiya da ke baiwa mazauna Kano damar gudanar da harkokinsu, tare da buƙatar gwamnati ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa a yankin Sabon Gari, musamman titunan New Road, Zungeru da Sarkin Yaki, da kuma taimakawa wajen kammala aikin gina gidan al’ummar Igbo.
Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce al’ummar Igbo na cikin muhimman ɓangarorin da ke bada gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Kano, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware naira biliyan 8 domin faɗaɗa titin Igbo Road da Hausa Road tare da sanya fitilun hasken titi, yayin da aikin New Road aka sake baiwa wani ɗan kwangila tare da ƙarin naira biliyan 3 domin kammala shi kafin watan Janairu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan ya ƙara da cewa gudummawar kuɗaɗen shiga daga al’ummar Igbo ta ƙaru da kusan kashi 70 cikin 100 sakamakon ingantuwar biyan haraji bisa son ran su, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare haƙƙin dukkan mazauna jihar ba tare da nuna bambancin ƙabila ko addini ba.
