Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 23 ga Nuwamban 2026, yayin wani taron tattaunawa da matasa, dattawa da shugabannin al’ummar Igbo a Legas.
An gudanar da taron ne a cibiyar al’adu ta Wole Soyinka da ke National Theatre, ƙarƙashin shirin ƙungiyar Ndigbo National Dialogue and Development Initiative.
Shugaban ƙasar ya ce duk da bambancin ra’ayoyin siyasa, gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani dukkan ‘yan Najeriya ba tare da nuna wariya ba.
Ya kuma nemi al’ummar Igbo da su mara masa baya a zaɓen 2027, tare da goyon bayan ɗan takarar gwamnan Legas na APC, Obafemi Hamzat, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar.
Tinubu ya yi bayanin cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin inganta harkokin ilimi, noma da kasuwanci, inda ya ambaci shirin bayar da rancen karatu na NELFUND da wasu tsare-tsaren bayar da rance.
A zaɓen 2023, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ne ya samu ƙuri’u mafi yawa a Jihar Legas, duk da cewa Tinubu ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a matakin ƙasa.
