Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yunƙurin tsige shi daga muƙaminsa zai jawo babbar illa ga jam’iyyar Democrats.
Trump ya yi wannan furuci ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan yiwuwar amfani da tsarin tsige shugaban ƙasa daga mulki.
Ya kuma yi iƙirarin cewa irin wannan mataki zai iya zama babban koma-baya ga jam’iyyar adawar ta Democrats.
