Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori shugabannin jam’iyyar ADC da Sanata David Mark ke jagoranta, tare da soke dukkan matakan da suka ɗauka a madadin jam’iyyar.
Hukuncin na nufin cewa matakan da wannan shugabanci ya ɗauka tun bayan karɓar ragamar gudanar da jam’iyyar ba su da ingancin doka, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ADC ke cikin shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
