Hon. Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, ya bayyana cewa zai fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a mako mai zuwa.
Nafiu Bala ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar TheCable, inda ya ce yana da ƙwarin gwiwar samun goyon bayan ’yan Najeriya a fafutukar siyasarsa.
Ya kuma bayyana cewa yana nazarin yiwuwar naɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓensa, muddin Atiku ya dawo jam’iyyar ADC yadda ya kamata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddamar shugabancin jam’iyyar ADC tsakanin ɓangaren Nafiu Bala da na tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.
A ranar 5 ga watan Nuwamban 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin David Mark, da kuma matakan da kwamitinsa ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da takarar Atiku.
Sai dai ɓangaren David Mark ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun, yayin da Atiku Abubakar ya jaddada cewa ba zai janye daga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.
