Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa ta kai hari kan wasu makamai da take zargin ana shirin safararsu zuwa ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, a yankin iyakar Syria da Lebanon.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta zargi Hezbollah da amfani da wasu yankuna wajen safarar makamai da gudanar da ayyukan da Isra’ila ke ɗauka a matsayin barazana ga tsaronta.
Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan soji domin kawar da duk wata barazana ga tsaron ƙasar.
Harin na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani wajen samarwa tsakanin Isra’ila da Hezbollah.
Yarjejeniyar ta tanadi janyewar sojojin Isra’ila daga wasu yankunan kudancin Lebanon, domin bai wa sojojin Lebanon damar karɓar iko da wuraren.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa sojojin Isra’ila na ci gaba da kasancewa a wasu yankunan kudancin Lebanon.
