Al’ummar Yarabawa mazauna Kano sun bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf, domin su zarce a wa’adin mulki na biyu.
Sarkin Yarabawa a Kano, Kabiyesi Murtala Alimi Otisese, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci shugabannin al’ummar Yarabawa zuwa gidan gwamnatin Kano, inda suka gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da sanar da matsayarsu kan zaɓen mai zuwa.
Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya godewa al’ummar Yarabawan bisa goyon baya da gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban Kano, tare da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa kowane ɓangare na al’umma kulawa ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.
Gwamnan ya kuma sake tabbatar da goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa akwai buƙatar mutunta tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, inda ya bayyana cewa Arewa ta amince Kudu ta ci gaba da riƙe shugabancin ƙasa har zuwa shekarar 2031, kafin mulki ya koma Arewa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, shi ma a nasa jawabin, Kabiyesi Murtala Alimi Otisese ya ce goyon bayan sake zaɓen Tinubu wajibi ne ga kowane bayerabe da ke Kano, tare da tabbatar da haɗin kan al’ummar wajen marawa Gwamna Abba baya, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin Kano domin samar da zaman lafiya da ci gaba.
