Gwamnatin Tarayya ta bai wa sabuwar Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Aminu Dabo (AD-UHS) da ke Kano lasisin fara gudanar da ayyukanta a matsayin jami’a mai zaman kanta a Najeriya.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), Farfesa Abdullah Yusuf Ribadu, ne ya miƙa takardar amincewar ga wanda ya kafa jami’ar, Arc. Aminu Dabo, a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026, a Abuja.
A cewar sanarwar jami’ar, an amince ta fara da tsangayar kimiyyar lafiya mai ɗauke da sassa takwas da shirye-shiryen karatu tara, ciki har da aikin jinya, lafiyar muhalli, lafiyar jama’a, kimiyyar abinci mai gina jiki da fasahar ɗaukar hotunan cikin jiki.
Farfesa Ribadu ya bayyana cewa lasisin na wucin gadi ne, inda NUC za ta sake tantance jami’ar bayan shekaru uku domin tabbatar da cika ƙa’idojin ilimi.
Ya ƙara da cewa an zaɓi Jami’ar Bayero Kano (BUK) domin bai wa sabuwar jami’ar shawarwari kan ɗaukar ƙwararrun malamai da gudanar da harkokin mulki.
A nasa jawabin, Aminu Dabo ya gode wa gwamnatin tarayya da NUC bisa amincewar, tare da alƙawarin samar da ingantaccen yanayin koyarwa da koyo.
