Yayin da duniya ke bikin ranar yaƙi da cutar siga a yau Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta horas da ma’aikatan lafiya 1,000 domin inganta kula da masu fama da cutar.
Kwamishinan Lafiyar Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa asibitoci 110 ne suka amfana da horon, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na gano cutar da wuri da rage illolinta.
Kwamishinan ya ce alkaluma sun nuna cewa kimanin mutum miliyan 589 ne ke fama da cutar siga a duniya, yayin da aka kiyasta yawan masu cutar a Najeriya da kashi bakwai cikin ɗari, da kuma kashi 7.5 cikin ɗari a Kano.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a da gwajin lafiya, tare da kira ga al’umma su riƙa tantance lafiyarsu domin gano cutar tun kafin ta haifar da matsaloli.
