Tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya musanta zargin ɓatan kuɗaɗe da yawansu ya kai kusan naira tiriliyan 210 a lokacin da yake jagorantar kamfanin.
Kyari ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa da ke gudanar da bincike kan zargin ɓatan kuɗaɗen.
Ya ce babu ko kwabo da aka sace ko ya ɓace a lokacin shugabancinsa, yana mai bayyana shirinsa na amsa tambayoyin duk wata hukuma da aka ɗora wa alhakin bincikensa.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, ya bayyana cewa an gayyaci Kyari ne domin jin ta bakinsa game da zarge-zargen.
Mele Kyari ya jagoranci NNPCL daga watan Yulin 2019 zuwa Afrilun 2025, bayan shafe sama da shekaru 30 yana aiki a masana’antar man fetur ta Najeriya.
