Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa jami’anta yayin da suke ƙoƙarin kashe gobara a yankin Gwarimpa da ke Abuja ranar Juma’a.
Kakakin hukumar, Barnabas Anyam, ya ce wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka jefi jami’an da duwatsu, lamarin da ya jikkata ɗaya daga cikinsu a kansa.
Ya bayyana cewa an garzaya da jami’in da ya jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar lafiya.
Anyam ya ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Galadima, inda aka kama wasu da ake zargi domin gudanar da bincike.
Shugaban hukumar a Abuja, Muhammad Anas, ya yi gargaɗin cewa za a ɗauki matakin doka kan duk wanda ya hana jami’an kashe gobara gudanar da aikinsu.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa ba jami’an agajin gaggawa haɗin kai domin kare rayuka da dukiyoyi.
