Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci bikin yaye ɗalibai karo na biyu na Kwalejin ’Yan Sandan Najeriya da ke Wudil, Jihar Kano.
Rahoton jaridar Justice Watch News ya bayyana cewa bikin zai haɗa da ƙaddamar da ɗaliban da suka kammala horo a matsayin jami’an rundunar ’yan sandan Najeriya.
Bikin na daga cikin muhimman ayyukan kwalejin wajen horas da sabbin jami’an tsaro domin gudanar da ayyukan tabbatar da doka da oda a ƙasar.
A watan Nuwamban 2025, kwalejin ta gudanar da bikin yaye ɗalibai na farko, inda aka yaye ɗalibai 1,199.
