Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dakatar da Sarkin Lame da ke Ƙaramar Hukumar Toro, Alhaji Aliyu Lame, bisa zarge-zargen rashin ɗa’a da amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Gwamnan Shawara Kan Yaɗa Labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026.
Sanarwar ta ce ana zargin Sarkin da tsoma baki cikin harkokin filaye, karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, da kuma katsalandan a ayyukan kamfanonin hakar ma’adinai.
Gwamnatin ta kuma kafa kwamitin bincike mai mutum 12, ƙarƙashin jagorancin tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Sani Mohammed, domin gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto cikin makonni uku.
Ta bayyana cewa an ɗauki matakin dakatarwar ne domin tabbatar da gudanar da bincike ba tare da tsangwama ba.
A halin yanzu, an ɗora wa Galadiman Lame, Alhaji Bala Gumau, alhakin kula da harkokin masarautar har zuwa kammala binciken.
Gwamnatin ta jaddada cewa zarge-zargen ba su tabbata ba, kuma za a bai wa Sarkin damar kare kansa.
