Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa rashin haɗin kai tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi na iya bai wa jam’iyyar APC damar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya bayyana hakan ne a cikin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a jiya Juma’a, inda aka tattauna kan siyasar kasar nan da kuma 2027.
Alhaji Lamido ya ce manyan ’yan siyasar ƙasar nan, ciki har da Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, sun fi mayar da hankali kan neman mulki maimakon magance matsalolin da ke addabar ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa yawan gwamnonin jam’iyyar APC, da kuma rabuwar kan ’yan adawa, na bai wa jam’iyyar damar samun rinjaye.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin yan siyasar ƙasar nan ke ƙara karkata zuwa farfaganda, yaɗa ƙiyayya da tunzura jama’a, musamman a Arewa, maimakon tattauna manufofin haɗin kai da kuma ci gaban ƙasa.
