Wasu al’ummar musulmi sun yi wa Tinubu ihu tare da rera taken adawa da shi bayan kammala sallar Juma’a a babban masallacin Shehu Shagari da ke Abuja.
Rahoton Premium Times ya ce wasu daga cikin mutanen sun rera taken “Ba mayi, ba ma so” da kuma “Tinubu Must Go” yayin da ayarin motocin shugaban ƙasar ke barin masallacin.
Wani ganau ya bayyana cewa jami’an tsaro sun hana mutane shiga masallacin bayan isowar Tinubu, tare da toshe hanyoyin da ke kaiwa wurin. An kuma hana masu ibada fita har sai shugaban ƙasar ya bar wurin.
Inda wasu majiyoyi suka danganta lamarin da tsaurara matakan tsaron da aka ɗauka, inda suka ce hakan ya fusata wasu masu ibada da aka tsare a wajen masallacin.
