Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa ƙasar na ci gaba da ɗaukar matakan ko-ta-kwana kan cutar Ebola, duk da cewa mutane 62 da aka sanya ƙarƙashin sa ido sun kammala kwanaki 21 ba tare da an tabbatar da kamuwa da cutar ba.
Daraktan cibiyar, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce mutane 13 daga cikin waɗanda aka sanya ƙarƙashin sa ido sun nuna wasu alamomin rashin lafiya, amma sakamakon gwaje-gwaje ya tabbatar ba su kamu da Ebola ba.
Haka kuma, an gwada wasu mutane bakwai da ake zargin sun kamu da cutar a jihohin Adamawa, Rivers, Borno, Legas da Ekiti, amma dukkan sakamakon gwaje-gwajen ya nuna babu wanda ya kamu.
Dakta Idris ya jaddada cewa kammala sa ido ba yana nufin an kawo ƙarshen barazanar cutar ba, musamman ganin rahotannin yaɗuwarta a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Ya ƙara da cewa NCDC ta ci gaba da gudanar da ayyukan sa ido da shirye-shiryen gaggawa domin kare lafiyar al’ummar Najeriya.
