Hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), reshen Kano, ta yi kira ga al’ummar da su taka rawar gani a zaɓen 2027, ta hanyar gujewa sayar da ƙuri’u su, rikicin siyasa da sauran abubuwan da ka iya kawo cikas ga gudanar da zaɓe cikin lumana.
Shugaban hukumar na ƙasa malam Lanre Isa Onilu ne ya bayyana hakan, lokacin da tawagar sa ta kaiwa ziyarar wayar da kan al’umma fadar Sarkin Rano.
Malam Lanre wanda Barrister Williams Manya Dogo, ya wakilta ya ce taron wayar da kan, wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar wajen faɗakarwa da wayar da kan al’umma musamman a ƙananan hukumomin Kano nauyin dake kan su na zabar shugabannin da ran su yake so domin dorewar zaman lafiya.
Malam Onilu ya buƙaci sarakunan gargajiya, malaman addini da shugabannin al’umma da su taimaka wajen wayar da kan jama’a muhimmancin yin rajistar zaɓe, karɓar katin zaɓensu na dindindin da amfani da shi wajen zaɓen shugabannin da suke so cikin lumana da bin doka.
Da yake jawabi, a wajen muƙaddashin shugaban hukumar ta NOA a Kano, Malam Nura Liman, ya ce hukumar za ta ci gaba da kai saƙonnin wayar da kan jama’a zuwa dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen isar da saƙonni ga al’umma.
A nasa ɓangaren, Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Ummaru, ya baiwa hukumar tabbacin cewa, za su ci gaba da tallafawa yunƙurin hukumar domin cimma nasarar da aka sanya a gaba.
