Malamin addinin Musulunci, Dr. Abdullah Gadon Kaya, ya yi gargaɗi ga wani mutum da ake zargin yana amfani da hoton rakumi da aka ƙirƙira ta hanyar AI wajen zagi da wallafa abubuwan batsa a kafafen sada zumunta.
Malamin ya bayyana hakan ne a cikin shirin Goron Juma’a, inda ya ce sun samu labarin cewa mutumin ɗan asalin Jihar Kano ne kuma Musulmi.
Dr. Gadon Kaya ya buƙaci mutumin ya dakatar da wannan ɗabi’a, yana mai cewa idan bai daina ba, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakin da doka ta tanada.
Ya kuma yi kira ga duk wanda ke da sahihan bayanai game da mutumin da ya sanar da hukumomin da suka dace.
