Babbar Kotun Tarayya da ke Kano sun tabbatar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bi umarnin kotu wajen ƙin wallafa sunan ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo.
Mai shari’a Samuel Amobeda ne ya bayar da umarnin wucin gadi a ranar 27 ga Oktoban 2026, bayan wasu mambobin jam’iyyar NDC uku sun shigar da ƙara suna ƙalubalantar tsarin zaɓen ɗan takarar gwamnan da mataimakinsa.
Umarnin ya hana INEC wallafa sunayen ƴan takarar NDC ko sauya jerin sunayen ƴan takarar gwamnan Kano har sai kotu ta saurari ƙarar.
A rahoton da jaridar Punch ta wallafa ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, takardun kotun sun tabbatar da cewa umarnin ne ya hana INEC saka sunan Gwarzo a sabon jerin ƴan takarar zaɓen 2027.
Sai dai wannan ba yana nufin an soke takarar Gwarzo ba, domin har yanzu kotun ba ta yanke hukuncin ƙarshe kan cancantar takararsa ba.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga Nuwamban 2026, bayan lauyan Gwarzo ya nemi kotu ta sanya shi cikin waɗanda ke da ruwa da tsaki a shari’ar.
