Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce kawo yanzu gwamnatin sa ta biya jimillar Naira biliyan 37 na kuɗaɗen bashin haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda ya gada daga gwamnatocin baya.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne lokacin da yake ƙara biyan Naira biliyan 5 na kuɗaɗen fansho da alawus-alawus na iyalan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da waɗanda suka rasu.
Gwamnan ya ce biyan haƙƙoƙi na daga cikin ƙoƙarin dawo da martaba da walwalar tsofaffin ma’aikatan waɗanda suka shafe shekaru suna yiwa jihar hidima ba tare da samun kuɗaɗensu ba.
Wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan da suka karbi hakkin na su sun yiwa Premier radio karin bayani kan halin da suka tsinci kan su bayan da suka karbi kuɗaɗen na su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na bayyana cewa, gwamnatinsa za ta kammala biyan dukkan bashin fansho da sauran haƙƙoƙin da ake bin ta kafin watan Afrilun 2027, tare da bullo da tsarin biyan kuɗaɗen duk wata maimakon tsarin da ake bi a baya.
