Majalisar Dattawan Najeriya ta bai wa sauran majalisun dokokin jihohi huɗu wa’adin zuwa Talata, 17 ga Nuwamba, domin miƙa rahotanninsu kan ƙudirin kafa rundunar ƴan sandan jihohi.
Shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce jihohi 32 sun riga sun amince da ƙudirin, wanda ya cika ƙa’idar amincewar kashi biyu bisa uku na jihohin Najeriya.
Ya ce za a ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin ko da sauran jihohin ba su miƙa rahotanninsu ba, kafin miƙa ƙudirin ga Shugaba Bola Tinubu.
Bamidele ya ƙara da cewa ƙudirin na da tanade-tanaden hana amfani da ƴan sandan jihohi wajen danniya ko cimma muradun siyasa.
