Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar ’yan sandan jihar, ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ’yan sanda, CP Adamu Bakori, bisa nasarar ceto shugaban APC na ƙaramar hukumar Rogo, Hon. Abdullahi Alasan Beli, bayan shafe kwanaki 68 a hannun masu garkuwa da mutane.
Da yake bayyana irin wahalhalun da ya fuskanta, shugaban APCn da aka ceto ya ce masu garkuwar sun riƙa yawo da shi wurare daban-daban wanda suka haɗa da Danja, Ikara da Giwa a jihar Kaduna, da kuma wasu sassan jihar Zamfara.
Sai dai da yake yiwa Gwamna Ƙarin bayani kan yadda suka ceto shi, kwamishinan ’yan sanda, CP Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne ta hanyar amfani da dabarun tsaro na musamman, tare da tabbatar da aniyar rundunar ’yan sandan Kano, na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da garkuwa da mutane da sauran laifukan da suka shafi tsaro.
Gwamnan ya umarci kwamishinan lafiya na jihar da ya tabbatar da cewa an baiwa wanda aka ceto cikakkiyar kulawar lafiya da taimakon tunani, a daga asusun gwamnatin Kano, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yabawa kwamishinan da sauran jami’an da suka taka rawa, musamman CSP Aliyu Muhammad Auwal, CSP Ado Muhammad Audi da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa.
