
Aminu Abdullahi Ibrahim
Bankin Duniya ya nuna damuwa kan yadda gwamnatocin jihohin Najeriya ke kashe kuɗaɗen shiga, yana mai cewa ba a ba fannin ilimi, kiwon lafiya da tallafin zamantakewa muhimmancin da ya dace ba.
Bankin ya ce duk da ƙarin kuɗaɗen da jihohi ke samu sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta aiwatar, kashe kuɗaɗen gine-ginen hanyoyi da sufuri ya ƙaru fiye da na muhimman ayyukan jin daɗin jama’a.
Babbar masaniyar tattalin arziki a ofishin Bankin Duniya na Najeriya, Gloria Joseph-Raji, ce ta bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, yayin ƙaddamar da rahoton BudgIT na shekarar 2026 kan yadda jihohi ke tafiyar da kuɗaɗensu.
Rahoton mai taken From Allocation to Impact: Rethinking State Spending Priorities ya yi nazari kan yadda jihohi ke amfani da kuɗaɗen da suke samu wajen samar da ayyukan more rayuwa.
Joseph-Raji ta ce kashe kuɗaɗen ilimi, kiwon lafiya da tallafin zamantakewa ya ƙaru, amma bai kai saurin ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen gine-ginen hanyoyi da sufuri ba.
Bankin ya kuma nuna cewa wannan yanayi ya fi tayar da hankali a jihohin da ke da ƙarancin ci gaba a fannin jin daɗin jama’a. Rahoton ya jaddada muhimmancin mayar da hankali kan ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma.
