Majalisar Dattawan Najeriya ta fara nazarin wani ƙudirin gyaran doka da zai tilasta wa asibitocin gwamnati da masu zaman kansu ba marasa lafiya agajin gaggawa domin rage mace-macen da ake samu sakamakon jinkirin kulawar likitoci.
Sanata Abdul’aziz ’Yar’adua, mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, ne ya gabatar da ƙudirin, wanda ya tanadi cewa dole ne asibitoci su tantance majiyyaci cikin mintuna 15 da isowarsa, sannan su fara ba shi agajin gaggawa cikin mintuna 30.
Ƙudirin ya samu karatu na biyu a Majalisar Dattawa, inda aka tura shi Kwamitin Lafiya domin ƙarin nazari kafin ɗaukar mataki na gaba.
Idan aka amince da ƙudirin kuma ya zama doka, zai ƙarfafa matakan tabbatar da cewa marasa lafiya na samun kulawar gaggawa a kan lokaci.
