Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da tsohon mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, da Balarabe Sa’idu Gani a matsayin sabbin kwamishinonin jihar.
An gudanar da bikin rantsuwar ne ranar Juma’a a gidan gwamnatin Kano, inda aka naɗa Sanusi Bature a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai, yayin da Balarabe Gani zai jagoranci Ma’aikatar Ma’adanai.
Gwamnan ya buƙaci sabbin kwamishinonin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, ƙwarewa da riƙon amana.
Ya kuma umarci Sanusi Bature da ya ƙarfafa wayar da kan jama’a, musamman kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi, yayin da ya buƙaci Balarabe Gani da ya mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin ma’adanai a jihar.
Abba Kabir Yusuf ya ce an zaɓi kwamishinonin ne bisa cancanta da ƙwarewarsu.
