Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi kwafin hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark ba.
Hukuncin kotun ya soke shugabancin jam’iyyar da wasu matakan da aka ɗauka wajen zaɓen ’yan takara gabanin babban zaɓen 2027.
INEC ta ce rashin samun cikakken kwafin hukuncin ne ya sa ba ta ɗauki matakin aiwatar da shi ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddama kan makomar shugabancin ADC da takarar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, gabanin zaɓen 2027.
