
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ministan sufuri na ƙasar Spain, Oscar Puente, ya yi murabus daga muƙaminsa bayan wani mummunan hatsarin jirgin ƙasa da ya yi sanadin mutuwar mutum 69.
Ministan ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama a ofis ba, bayan faruwar manyan haɗurran jiragen ƙasa guda biyu a ƙasar cikin ƙasa da shekara guda.
Hatsarin na baya-bayan nan ya faru ne a layin dogo tsakanin Madrid da Seville, inda wani jirgin ƙasa mallakar gwamnatin ƙasar ya yi karo da wani jirgin ƙasa mai zaman kansa.
Bayanai sun nuna cewa jirgin ya yi karo da wani jirgin da ke tsaye, bayan samun matsala a tsarin siginar da ke kula da zirga-zirgar jiragen.
An ce ma’aikatan kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa daga babban birnin Madrid ne suka ba jirgin izinin ci gaba da tafiya, duk da matsalar da aka samu a siginar.
Gwamnatin Spain ta sanar da ɗaukar matakan inganta tsaron layukan dogo, ciki har da amfani da fasahar basirar na’ura mai kwakwalwa wajen gano matsaloli da rage kuskuren ɗan Adam. Ta kuma sanar da tallafin Yuro miliyan 30 ga waɗanda suka rasa ‘yan uwansu da sauran waɗanda hatsarin ya shafa.
