Gwamnatin Kano ta tabbatarwa da mazauna ƙananan hukumomin Danbatta, Minjibir da Makoda cewa za’a dawo da cikakken samun da ruwan sha mai tsafta a yankunan su, nan da mako mai zuwa.
Kwamishinan albarkatun ruwa na Kano, Dr. Dahiru Hashim, ne ya bayyana hakan bayan duba tashar samar da ruwa ta Thomas da ke ƙaramar hukumar Danbatta, biyo bayan sake fara aiki da tashar ta yi.
Dr. Hashim ya ce sake fara aikin da tashar ta yi zai inganta samun ruwan sha mai tsafta a ƙananan hukumomin uku, inda ya bayyana cewa za’a ƙara yawan ruwan da tashar ke samarwa daga lita dubu 650 a kowace rana zuwa lita miliyan ɗaya cikin ƴan kwanaki masu zuwa.
Da yake jawabi a wajen, mukaddashin shugaban hukumar samar da ruwan sha da Inganta tsaftar muhalli a karkara ta Kano, KASSTOWA, Injiniya Sani Bala Danbatta, ya ce an kafa tashar ta Thomas ne a shekarar 1976 domin samar da ruwan sha ga al’ummomin karkara da kuma tallafawa ayyukan ban-ruwa.
Injiniya Danbatta ya kuma yi kira ga jama’a da su sanya ido wajen kare kadarorin gwamnati daga ɓata gari, tare da kai rahoton duk wani abin da suke zargi ga hukumomin da abin ya shafa.
KUK
