Aƙalla mutum 16 ne suka rasa rayukansu, sama da 12 kuma suka jikkata sakamakon wata fashewa da ta auku a wata masana’antar sarrafa ƙarafa da ke lardin Izmir a yammacin Turkiyya.
Gwamnan lardin ya ce fashewar ta faru ne bayan wata na’urar daga kaya ɗauke da tukunya ta kife, lamarin da ya sa wasu kayayyaki suka faɗa a inda ake narkar da ƙarafa.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce an kaddamar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.
A halin yanzu, jami’an ceto da na agaji na ci gaba da gudanar da ayyukan neman waɗanda abin ya shafa da kuma ceto waɗanda ka iya kasancewa a karkashin baraguzan ginin.
